Isa ga babban shafi

Van Nistelrooy zai fara aikin horaswa a sabuwar kakar wasa

Tsohon dan wasan Manchester United da Netherlands, Ruud van Nistelrooy, zai karbi aikin horas da kungiyar PSV Eindhoven da ke kasarsa Netherlands daga kakar wasa mai zuwa.

Tsohon dan wasan Netherlands, da yayi fice a kungiyoyin Manchester United da Real Madrid Ruud van Nistelrooy.
Tsohon dan wasan Netherlands, da yayi fice a kungiyoyin Manchester United da Real Madrid Ruud van Nistelrooy. © REUTERS/Bernadett Szabo
Talla

Cikin sanrwar da ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta PSV ta ce za ta yi sallama da kocinta na yanzu Roger Schmidt a karshen kakar wasa ta bana.

Van Nistelrooy, wanda ya taka leda a PSV tsakanin shekarun 1998 zuwa 2001, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin horas da kungiyar ne har zuwa shekarar 2025.

Van Nistelrooy, wanda ya yi ritaya daga buga wasa a shekarar 2012, ya zura kwallaye 35 a wasanni 70 da ya buga wa kasarsa Netherlands.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.