Isa ga babban shafi
Wasanni

Mai yiwuwa Suarez ya koma tsohuwar kungiyarsa

Mai yiwuwa dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez, ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Ajax dake Netherlands, bayan da makomarsa a Barcelonan ta shiga hali na rashin tabbas, a dalilin lallasa su da kwallaye 8-2 da Bayern Munich ta yi a gasar zakarun Turai.

Dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez
Dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez REUTERS/Albert Gea/File Photo
Talla

Tuni dai Barcelona ta sanya ‘yan wasanta da shekarunsu suka tura a kasuwa, wadanda ake kyautata zaton Suarez na cikinsu, la’akari da cewar shekara guda kawai ta rage a yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar, kuma a yanzu haka babu batun tattaunawa don kara wa'adinta.

Bayanai sun ce Ajax ta soma shirin mikawa Suarez tayin yi mata kome bayan shafe shekaru 9 da rabuwarsu.

A shekarar 2007 Suarez ya soma haskawa Ajax, inda ya shafe shekaru 3 da rabi, tare da ci mata kwallaye 111 a wasanni 159 da ya buga mata, lafin daga bisani ya koma Liverpool a 2011.

Yanzu haka kuma, Suarez ya ci wa Barcelona kwallaye 195 a wasanni 292 da ya buga mata, tun bayan soma haskawa a kungiyar daga watan Yulin 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.