Isa ga babban shafi
Olympics

Tokyo: An yi bikin rufe gasar Olympics ta bana

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, Thomas Bach, ya jagoranci rufe wasannin motsa jikin na Olympics na Tokyo 2020 da kasar Japan ta karbi bakunci.

Yadda aka yi bikin kawo karshen gasar Olympics a babban filin wasa na birnin Tokyo a kasar Japan.
Yadda aka yi bikin kawo karshen gasar Olympics a babban filin wasa na birnin Tokyo a kasar Japan. © AP - Kiichiro Sato
Talla

Bikin na ranar Lahadi ya kawo karshen gasar wasannin motsa jiki mafi fuskantar kalubale da aka gani, biyo bayan bayan jinkirta gudanar ta da aka yi saboda annobar Korona tsawon shekara guda, gami da fuskantar barazanar soke ta har zuwa cikin wannan shekara.

Tuni dai aka mika tutar Olympics ga Magajin Garin Paris Anne Hidalgo, kasancewar babban birnin na Faransa ne zai karbi bakuncin gasar a shekarar 2024.

Yadda aka yi bikin karbar tutar gasar Olympics ta 2024 a birnin Paris na Faransa.
Yadda aka yi bikin karbar tutar gasar Olympics ta 2024 a birnin Paris na Faransa. AP - Francois Mori

Kasar Amurka ce ta zama zakara a gasar Olympics ta bana, bayan lashe lambar yabo ta Zinare 39, Azurfa 41 da kuma Tagulla 33, lambobin yabo 113 a jumlace.

China da ta zo kasa ta biyu a gasar ta Olympics, ta lashe jumillar lambobin yabo 88 da suka hada da Zinare 38, Azurfa 32 da Tagulla 18, yayin da mai masaukin baki Japan ta zo ta uku bayan lashe lambobin yabo 58, da suka kunshi Zinare 27, Azurfa 14 da kuma Tagulla 17.

'Yan wasan kwallon Volley Ball na Amurka ajin mata yayin murnar lashe lambar yabo ta Zinare bayan doke takwarorinsu na Brazil a gasar Olympics da Japan ta karbi bakunci.
'Yan wasan kwallon Volley Ball na Amurka ajin mata yayin murnar lashe lambar yabo ta Zinare bayan doke takwarorinsu na Brazil a gasar Olympics da Japan ta karbi bakunci. © US Today

Sauran kasashen da suka taka rawar gani sun hada da Birtaniya mai Zinare 22 abinda ya bata damar zama ta 4, sai kuma ‘yan wasan kasar Rasha da suka fafata wasannin na Olympics a matsayin masu zaman kansu, da suka kare gasar a mataki na 5, bayan lashe Zinare 20, sai Australia mai zinare 17.

Kasashen Netherlands, Faransa, Jamus, da kuma Italiya da ke matsayin na 7, 8, 9 da kuma 10, dukkaninsu sun samu lashe lambobin yabon Zinare goma-goma, inda aka banbance a adadin lambobin Azurfa da Tagulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.