Isa ga babban shafi
GASAR-OLYMPICS

Brazil ta lashe zinaren kwallon kafar maza a Olympics

Kasar Brazil tayi nasarar lashe zinari a gasar kwallon kafar Olympics bangaren maza da aka gudanar a Tokyo sakamakon nasarar da ta samu akan Yan wasan Spain da ci 2-1.

 Malcom bayan jefawa Brazil kwallon ta na biyu a gasar Olympics
Malcom bayan jefawa Brazil kwallon ta na biyu a gasar Olympics REUTERS - AMR ABDALLAH DALSH
Talla

Wannan nasarar ta baiwa Brazil damar samun zinari da kuma kare kambin ta da ta samu shekaru 4 da suka wuce lokacin da ta samu irin wannan nasarar.

Tawagar Yan wasan Brazil da suka lashe zinare
Tawagar Yan wasan Brazil da suka lashe zinare Anne-Christine POUJOULAT AFP

Brazil ta fara jefa kwallo a karawar ta yau ta hannun Matheus Cunha, yayin da Spain ta farke cin ta hannun Mikel Oyarzabal, abinda ya sa wasan ya zarce zuwa Karin lokaci bayan kamala shi da ci 1-1.

A minti 108 Malcolm da ya shiga canji ya jefawa Brazil kwallon ta na biyu, abinda ya bata nasarar lashe wasan.

Tawagar Yan wasan Brazil da suka lashe zinare
Tawagar Yan wasan Brazil da suka lashe zinare AP - Fernando Vergara

Wannan nasarar ta kara yawan irin nasarorin da 'dan wasan Brazil Dani Alves mai shekaru 38 ya samu, a matsayin na kaftin ko kuma jagoran 'Yan wasan da suka taka gagarumar rawa a wasannin.

A shekarar 2016 Neymar Jnr ne ya jagoranci tawagar Yan wasan Brazil wajen lashe zinaren gasar, kuma tun daga shekarar 1988 babu wata kasar Turai da ta samu nasara akan kasar a wasannin Olympics.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.