Isa ga babban shafi
Wasanni

Sevilla ta lashe kofin gasar Europa na 6

Kungiyar Sevilla ta lashe kofin kasar Europa karo na 6, bayan doke Inter Milan da kwallaye 3-2 a wasan karshen da suka fafata daren jiya a birnin Cologne dake Jamus.

Yan wasan Sevilla bayan samun nasarar lashe kofin gasar Europa a birnin Cologne.  21/8/2020.
Yan wasan Sevilla bayan samun nasarar lashe kofin gasar Europa a birnin Cologne. 21/8/2020. AFP
Talla

Nasarar dai ta baiwa Sevilla damar lashe gasar ta Europa fiye da kowace kungiya da tazarar kofuna 3.

Inter Milan ta zura kwallayenta ne ta hannun ‘yan wasanta Diego Godin da Romelu Lukaku, yayin da Sevilla ta jefa kwallayenta ta hannun dan wasanta Luuk de Jong, sai kuma kwallo ta uku da Lukaku ya jefawa gidansu kwallo bisa kuskure.

Yayin tsokaci kan nasarar da suka samu, kocin Sevilla Julen Lopetegui, yace ko kadan a yanzu baya tuna matsalolin da ya fuskanta yayinda ya horas da tawagar kwallon kafar Spain da kuma kungiyar Real Madrid, wurare biyun da aka sallame shi ba tare da ya dauki lokaci yana jagorantarsu ba.

Lopetegui ya jagoranci Sevilla wajen lashe gasar Europa ta bana ne, a kakar wasa ta farko da ya soma horas da kungiyar, yayin da shi kuma kocin Inter Milan Antonio Conte ya samu nasarar jagorantar kungiyar zuwa matakin wasan karshe a gasar zakarun Turan ta Europa, karo na farko cikin shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.