Isa ga babban shafi
UEFA

Sevilla ta lashe Europa League na 2016

Sevilla ta lashe kofin Europa league bayan ta doke Liverpool ci 3 da 1 a fafatawar da suka yi jiya a filin St Jacob Perk a Basel kasar Switzerland. Karo na uku ke nan da Sevilla ke lashe kofin a jere da jere.

Sevilla ta lashe Europa League karo uku da jere da jere
Sevilla ta lashe Europa League karo uku da jere da jere REUTERS
Talla

Lashe kofin dama ce ga Sevilla na tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai a kaka mai kamawa.

Liverpool ce ta fara jefa kwallo a raga amma bayan dawo wa hutun rabin lokaci Sevilla ta jefa kwallaye uku a raga.

A karon farko kuma hukumar UEFA ta yi amfani da fasahar tantance kwallo a raga a wasan karshe na gasar Europa da aka gudanar tsakanin Sevilla da Liverpool.

Liverpool ta yi harin lashe kofin ne bayan shafe shekaru 15, tun lokacin da ta doke Deportivo Alaves in 2001.

Karo na biyar a jere da jere ke nan kocin Liverpool Jurgen Klopp ke shan kashi a wasan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.