Alves zai fice Barca
Alamu na nuna cewa Dani Alves na Brazil na kan hanyar ficewa Barcelona bayan ya ki amincewa da tayin da kungiyar ta yi masa na tsawaita kwantaraginsa idan kwangilar shi ta kawo karshe. Yanzu haka manyan kungiyoyin Turai na neman dan wasan da suka hada da PSG da Manchester United.
Wallafawa ranar:
Wakilinsa Dinorah Santana ya ce lura da yadda dan wasan ke buga wa Barcelona wasa a ko yaushe, yana bukatar karin kudade fiye da yadda ya ke karba a yanzu.
Kofuna 16 Alves ya lashe a Barcelona tun zuwansa daga sevilla a 2008, kuma ficewarsa a kaka mai zuwa babbar baraka ce ga kungiyar saboda takunkumin da FIFA ta kakaka ma ta na sayen ‘yan wasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu