Isa ga babban shafi
Premier League

Drogba ya dawo Chelsea

Didier Drogba ya sake kulla yarjejeniyar shekara guda da tsohuwar Kungiyar shi Chelsea bayan kwantaraginsa ta kawo karshe a Galatasaray ta Turkiya. Tuni Mourinho yace yana bukatar dan wasan wanda ya kwashe shekaru takwas a Chelsea kafin ya koma taka leda a China. 

Dan wasan Cote d'Ivoire Didier Drogba
Dan wasan Cote d'Ivoire Didier Drogba Reuters
Talla

Kafin kulla yarjejeniyar, Kocin Chelsea Jose Mourinho yace Didier Drogba dan wasan Chelsea ne.

Mourinho yace suna son lashe kofuna kuma kowa ya san Drogba masanin raga ne a kwallon Turai, wanda ya saba da gasar Premier.

Kafin ya koma kasar China, Drogba mai shekaru 36 ya jefa wa Chelsea kwallaye 157 a shekaru Takwas da ya kwashe da kungiyar.

A watan Janairun 2013 ne Drogba ya koma Galatasaray daga kungiyar Shanghai Shenua ta China.

Kafofin yada labaran Birtaniya sun ruwaito cewa Drogba zai dawo Chelsea ne domin fara aikin horar da ‘Yan wasa, amma Mourinho yace dan wasan na Cote d’Ivoire zai dawo ne don ya taka wa Chelsea leda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.