Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

La liga ta fi Premier dadi-Bale

Tsadadden dan wasan kwallon kafa a duniya Gareth Bale da Real Madrid ta saya daga Tottenham akan kudi Fam miliyan 85.3 yace gasar La liga a Spain ta fi dadi fiye da gasar Premier ta ingila saboda yadda gasar ta kunshi manyan zaratan ‘Yan wasa na duniya.

Gareth Bale, na Real Madrid
Gareth Bale, na Real Madrid
Talla

Bale wanda zai fara hammaya da Rodriguez domin rike matsayinsa a Real Madrid yace duk dan wasa a Premier muradinsa ya zo Spain.

A bana Real Madrid da Barcelona sun zuba zunzurutun kudi suka yo cefanen wasu zaratan ‘Yan wasa, inda Real ta saye James Rodriguez daga Monaco yayin da Barcelona ta saye Luis Suarez daga Liverpool dukkaninsu maciya raga.

Yanzu dai sai Bale ya yi gaske a Real Madrid saboda zuwan Rodriguez wanda ya fi kowa zira kwallaye a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.