Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Argentina ta doke Holland

Kasar Argentina ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar cin kofin duniya a Brazil, bayan ta doke Holland a bugun Fanariti, ci 4 da 2. Yanzu Argentina zata hadu ne da Jamus a wasan karshe a ranar Lahadi.

Mai tsaron gidan Argentina Sergio Romero yana kabe Fanariti a gasar cin kofin duniya a Brazil
Mai tsaron gidan Argentina Sergio Romero yana kabe Fanariti a gasar cin kofin duniya a Brazil Reuters
Talla

Mai tsaron gidan Argentina Romero wanda ke kamawa kungiyar Monaco kwallo a Faransa shi ne ya kabe kwallayen Ron Vlaar da Wesley Sneijder a bugun Fanalti, wanda ya ba Argentina nasar tsallake zuwa zagayen karshe a karon farko tsawon shekaru 24 a tarihin gasar cin kofin duniya.

'Yan wasan Argentina Lionel Messi, Pablo Zabaleta , Martin Demichelis , Marcos Rojo , Lucas Biglia , Rodrigo Palacio , Javier Mascherano, Ezequiel Garay and Sergio Aguero.
'Yan wasan Argentina Lionel Messi, Pablo Zabaleta , Martin Demichelis , Marcos Rojo , Lucas Biglia , Rodrigo Palacio , Javier Mascherano, Ezequiel Garay and Sergio Aguero. REUTERS/Dylan Martinez/Files

Jamus da ta caccasa Brazil ci 7-1 zata hadu ne yanzu da Argentina a ranar Lahadi a wasan karshe a filin wasa na Maracana a birnin Rio de Jeneiro.

Jamus dai ta taba doke Argentina a wasan karshe da kasashen biyu suka fafata a shekara ta 1990 a Birnin Rome.

Haka kuma Argentina ta taba doke Jamus ci 3-2 a wasan karshe a Mexico a shekara ta 1986.

Amma a ranar Lahadi mace mai ciki ce ba’a san mai za ta Haifa ba.

Matsayi na uku.

Brazil da ke juyayin kashin da ta sha a hannun Jamus, a ranar Assabar ne zata nemi matsayi na uku tsakaninta da Holland da Argentina ta doke.

Kocin Holland, Louis van Gaal yace neman na uku bata lokaci ne, domin babu muhimmanci a karawar.

Sabon kocin na Manchester United, yace tuntuni ya dace ace FIFA ta soke karawar neman na uku domin karin takaici ne da wahala ga ‘Yan wasan da aka haramtawa kai wa zagayen karshe.

A yau Litinin dai batun rashin nasarar da ‘Yan wasan Orange na Holland suka samu shi ne ya mamaye jaridun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.