Isa ga babban shafi
Brazil 2014

An yi waje da Spain a Brazil

Kasar Spain ta sake shan kashi a hannun Chile ci 2 da 0, wanda hakan ya tabbatar da an yi waje da kasar tun a zagayen farko, Spain da ta lashe kofin gasar cin kofin duniya a Afrika ta kudu a shekara ta 2010.

Zaratan 'Yan wasan Spain David Silva, Sergio Busquets, Diego Costa, Andres Iniesta da Xabi Alonso da suka sha kashi a Brazil
Zaratan 'Yan wasan Spain David Silva, Sergio Busquets, Diego Costa, Andres Iniesta da Xabi Alonso da suka sha kashi a Brazil Reuters
Talla

Holland kuma ta doke Australia ci 3 da 2, kuma Holland ce ke jagorancin rukuninsu na B.

A rukunin B, Holland da Chile sun tsallake zuwa zagaye na biyu, bayan sun samu nasara a wasanni biyu da suka buga a Brazil.

Tawagar 'Yan wasan Chile da suka doke Spain
Tawagar 'Yan wasan Chile da suka doke Spain Reuters

Kashin da Spain ta sha a Brazil, shi ke nuna matsayinta ya kawo karshe, duk da tarin zubin zaratan ‘Yan wasan da kasar ta tara.

An shafe lokaci mai tsawo Spain tana matsayin ta farko a fagen kwallon kafa a duniya bayan ta lashe kofin Turai a 2008 da kofin gasar cin kofin Duniya a 2010 tare da sake lashe kofin Turai a 2012.

Sai dai ba wannan ne karon farko ba da kasar da ke rike da kofin duniya ta fice gasar tun a zagayen farko, domin hakan ta taba faruwa da Italiya a 1950 da 2010, haka ma Brazil a 1966 da Faransa a 2002.

Kafin dai Spain ta koma gida zata sake karawa da Australia wacce ita ma aka yi waje da ita a gasar.

Batun ficewar Spain a gasar cin Kofin Duniya a Brazil shi ne ya mamaye kanun labaran Jaridun wasanni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.