Isa ga babban shafi

An nada Luis Van Gaal a matsayin sabon kocin Manchester United

Kungiyar Manchester United ta nada kocin kasar Netherland ko kuma Holland Luis Van Gaal a matsayin sabon kocin da zai horar da ‘yan wasan kungiyar. Sannan a daya bangaren an nada Ryan Giggs, wato fitaccen dan wasan kungiyar a matsayin mataimakin Van Gaal.  

Sabon kocin Manchester United, Luis Van Gaal
Sabon kocin Manchester United, Luis Van Gaal eurosport.com
Talla

Dan shekaru 62, Van Gaal ya saka hanu ne a kan kwantirakin shekaru uku, shine kuma wanda zai maye gurbin David Moyes wanda kungiyar ta sallama a watan da ya gabata.

Sai dai sabon kocin ba zai kama aiki ba, har sai an kammala gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil, domin shi zai jagoranci ‘yan wasan Netherland.

Shi dai Van Gaal, mutum ne da aka san shi da tabbatar da da’a a wajen tafiyar da harkokinshi, wanda a bangaren aikinshi kuma, ya horar da kungiyar Ajax dake kasar ta Holland, da Barcelona ta kasar Spain da kuma Bayern Munich ta kasar Jamus.

Kuma wani abin lura anan shine, Van Gaal shi zai fara zama koci na farko da zai horar da kungiyar ta Man U. wanda kuma ba daga yankin Birtaniya yake ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.