Fafatawar karshe a Premiership
A ranar Lahadi ne za’a yi fafatawar karshe a gasar Premiership ta Ingila, kuma za a gudanar da dukkanin wasannin a lokaci guda tare da tantance kungiyar da zata lashe kofin gasar tsakanin Manchester City da Liverpool.
Wallafawa ranar:
Manchester City tana neman maki guda ne kacal ta lashe kofin a karawar karshe da West Ham, kuma idan har City ta yi kunnen doki, Liverpool na iya lashe kofin idan ta samu tazarar kwallayen da zata zira a karawar karshe.
Haka kuma Liverpool na iya lashe kofin a karon farko tun 1990 idan ta doke Newscatle kuma City ta sha kashi a hannun West Ham.
Manchester United, na iya shiga gasar Turai ta Europa idan har Aston Villa ta doke Tottenham, amma sai idan United ta doke Southampton kafin ta tsallake da yawan kwallaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu