Isa ga babban shafi
Wasanni

Ribery ba zai buga wasan Bayern da Arsenal

Kulob din Bayern Munich ya ce shahrarren dan wasansa Franck Rebery ba zai samu damar bugawa a kararwa da za a yi tsakanin Bayern da kuma Arsenal a gasar zakarun nahiyar Turai zagaye na farko da za a buga tsakanin kulob din 2 a ranar 19 ga wannan wata na Fabarairu.

Franck Ribery, dan wasan Bayern Munich
Franck Ribery, dan wasan Bayern Munich REUTERS/Fadi Al-Assaad
Talla

Ribery dai na farfadowa ne daga jinyar da yake yi bayan da aka yi masa aiki a ranar 6 ga wannan wata sakamakon raunin da ya sama a lokacin da yake buga wani wasa.
A ranar ta 19 ga wannan wata, ‘yan wasan Bayern Munich za su tattaki zuwa London domin karawa da ‘yan Arsenal, kafin su kuma ‘yan Arsenal su yi irin wannan tattaki zuwa Jamus domin karawa da su a ranar 11 ga watan Maris mai zuwa.

Kwallon kafar Ingila

A ci gaba da wasan Premier a kasar Ingila kuwa, a yammacin yau talata akwai wasanni da dama da ake shirin bugawa, inda Cardiff za ta karbi bakuncin Aston Villa, Southampton za ta yi tattaki ne zuwa Hull, sai Westham da za ta karbi Norwich, yayin da Westbrom ke shirin kece reni da Chelsea mai jagorantar teburin gasar Premier a halin yanzu.

Olympics

A kasar Rasha yau an shiga rana ta 4 a ci gaba da wasannin Olympics na hunturu, yayin da ‘yan wasa ke daukar lambobin yabo a matakai daban daban
A halin yanzu dai kasar Cananda ce jagorantar sauran kasashen ta fannin yawan kyaututuka, inda take da kyaututuka guda 7, wato 3 na zinari, azurfa 3 da kuma kyauta 1 ta ta tagula.
Netherland na a matsayin ta biyu ita ma da kyaututuka 7, zinari 3, azurfa 2 sai kuma tagula 2.
Norway kuwa na a mtsayin ta uku ita ma da maki 7, zinari 3 azurfa 2 da kuma tagula 4. Kasashe kamar Faransa na can a matsayin ta 8 da kyaututuka guda 2, zinari 1 tagula 1, yayin da Birtaniya ke can a matsayin ta 18 da kyauta 1 ta tagula.
Za a ci gaba dai da wasannin har tsawon kwanaki 16 a Sochi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.