Isa ga babban shafi
Wasanni

An wanke Karim Benzema da Franck Ribery daga zargin lalata

Wata kotun birnin Paris ta yi watsi da zargin da ake wa ‘yan wasan kasar Faransa su 2, wato Karim Benzema da Franck Ribery, da aka zarga da yin lalata da wata karuwa mai kananan shekaru mai suna Zahia Dehar. Kotun ta kuma yi watsi da zargin da aka yi wa wani surukin Ribery, sai dai ta yanke wa wasu mutanen 5, hukuncin daurin da ya kama daga watanni 3 zuwa shekara guda, saboda samun su da laifin kawalci.A shekarar 2009 aka zargi Ribery da yi lalata da Zahia yayin da shi kuma Benzema a sheakarar 2008, duk lokacin tana karamar yarinya.Dokokin Faransa sun hana yin lalata da matan da basu kai shekaru 18 ba, don a biya su kudi. 

Franck Ribéry tare da Karim Benzema, kotu ta wanke su
Franck Ribéry tare da Karim Benzema, kotu ta wanke su FP PHOTO / FRANCK FIFE
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.