Isa ga babban shafi
Tennis

Sharapova ta hauro Matsayi na biyu a jerin jaruman Tennis na Duniya

Maria Sharapova ta Rasha ta hauro zuwa matsayi na biyu a jerin jaruman Tennis na Duniya inda ‘yar wasan ta ke takewa wa Serena Williams baya da ke matsayi na daya a Duniya. Sharapova ta samu haurowa ne bayan lashe kofin Indian Wells.

Maria Sharapova ta Rasha
Maria Sharapova ta Rasha Reuters/Nir Elias
Talla

Maria Sharapova ta karbe matsayin Victoria Azarenka ne ta Belarus wacce ta koma a matsayi na uku bayan kwashe watanni tana a matsayi na daya a duniya.

Jerin sunayen Jaruman Tennis daga matsayi na daya zuwa na goma.

1. Serena Williams (Amurka)

2. Maria Sharapova (Rasha)

3. Victoria Azarenka (Belarus)

4. Agnieszka Radwanska (Poland)

5. Li Na (China)

6. Angelique Kerber (Jamus)

7. Sara Errani (Italiya)

8. Petra Kvitova (Czech)

9. Caroline Wozniacki (Denmark)

10. Samantha Stosur (Autralia)
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.