Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Nadal ya dawo fagen wasan Tennis bayan watanni bakwai

Dan wasan Tennis na kasar Spain, Rafael Nadal ya dawo fagen wasan kwallon Tennis watanni bakwai bayan an fitar da shi daga gasar Wimbledon. Nadal ya fara wasa da wani wasan tada tsimi na hadin gwiwa wanda suka buga tare da Juan Monaco dan kasar Argentina inda suka fafata da Frantisek Cerman da Lukas Dlouhy, suka kuma samu nasara a kansu da ci 6-3,6-2. 

Rafael Nadal
Rafael Nadal REUTERS/Toby Melville
Talla

Sau 11 Nadal yana lashe Grand Slams daban-daban kuma bai samu damar shiga gasar Australian Open da aka kammala a kwana-kwanan nan ba, wanda hakan yasa ya koma matsayin na biyar a duniya a maimakon na hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.