Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

An rufe kasuwar ‘Yan wasa, Beckham ya koma PSG

A daren Alhamis ne aka rufe kasuwar nikikayyar ‘Yan wasa a Turai kuma wasu kungiyoyin sun yi cefanen ‘Yan wasan a ranar karshe. David Beckham na Ingila ya koma kungiyar PSG bayan kulla yarjejeniyar watanni biyar.

David Beckham, da Shugabannin PSG
David Beckham, da Shugabannin PSG REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Beckham ya lashe kofin Premier da La liga da kofin League din Amurka a Manchester United da Real Madrid daLos Angeles Galaxy. Kuma An bayyana David Beckham ya mallaki kudi da suka kai Pam miliyan 190.

Batun David Beckham ne ya mamaye kanun labaran Jaridun Birtaniya a yau inda suka ce duk da yawan shekarun dan wasan amma har yanzu yana cikin fitattun ‘yan wasa a Duniya.

Bayan Beckhma akwai cinikin Mario Balotelli wanda ya koma taka kwallo a AC Milan daga Manchester City akan kudi Fam miliyan 19.

Akwai CHRISTOPHER SAMBA wanda QPR ta saya akan kudi Fam Miliyan 12.5 daga Anzhi Makhachkala ta Rasha.

Akwai DANIEL STURRIDGE wanda Chelsea ta sayar wa Liverpool akan kudi da aka ruwaito sun kai Fam Miliyan 12.

Sai WILFRIED ZAHA na Cote d’Ivoire wanda Manchester United ta saya daga Crystal Palace akan kudi Fam Miliyan 10.

Chelsea kuma ta saye Demba Ba daga Newcastle United akan kudi Fam Miliyan Bakwai.

Akwai kuma Joe Cole wanda ya koma West Ham daga Liverpool.

Kungiyar Arsenal kuma a daren jiya ta kammala cinikin Nacho Monreal daga Malaga akan Kudi Fam Miliyan 8.3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.