Isa ga babban shafi
Olympic

‘Yan wasan Olympic Musulmai sun shiga rudani saboda Azumi

Kimanin Musulmai 3,500 ne suka shiga wasannin Olympics da za’a gudanar a birnin London a bana kuma sun shiga wasannin ne a dai dai lokacin da Al’ummar Musulmin duniya ke gudanar da azumin watan Ramadan inda za su kauracewa cin Abinci da Sha da saduwa da iyali tsakanin safiya zuwa faduwar Rana.

Wani Musulmi yana Salla a filin guje guje.
Wani Musulmi yana Salla a filin guje guje. By Stéphanie TROUILLARD
Talla

Yawancin ‘Yan wasan sun ce za su dakatar da yin Azumi a lokacin Wasannin domin samun kuzari, amma za su ranka Azumin idan sun koma gida.

Sai dai kuma wasunsu da dama sun ce za su ci gaba da gudanar da Azuminsu domin Ibada ce da ta zama Tilas a gare su.

Methkal Abu Drais dan kasar Morroco kuma zakaran tseren gudun Marathon sau hudu yace ya yi kokarin daukar Azumi bayan isar shi birnin London a lokacin da ya ke horo, amma ya gano ci gaba da yin Azumin abu ne mai wahala a wasannin Olympics.

Kodayake wasu daga cikin tawagar kasar Morroco sun ce za su ci gaba da gudanar da Azuminsu domin Ibada ce da ta zama dole.

A cikin Tawagar Jamhuriyyar Nijar, yawancin ‘Yan wasan sun daure da Azuminsu illa dan wasa Zakari Gourouza wanda ya ajiye Azumi har sai an kammala wasannin.

Akwai dai Sassauci da aka yi wa Musulmi game da ajiye Azumi idan suna cikin rashin Lafiya ko kuma lokacin tafiya.

Wasu ‘Yan wasan sun ce sun ajiye Azumi ne domin dogara da sassaucin da aka yi wa Matafiyi saboda zamansu baki a birnin London.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.