Isa ga babban shafi
Olympic

Shugabannin duniya za su yi tururuwa a bukin bude wasannin Olympic a London

Daruruwan manyan mutane ne da shugabannin kasashen duniya za su kai ziyara birnin London a ranar Jum’a da za’a bude wasannin Olympic, kuma manyan bakin sun hada da Angelina Jolie ‘Yar Fim din Amurka da kuma uwar gida Michelle Obama da Sarkunan kasashe da dama.

Wani Jirgin Jami'an tsaro da ke shawagi a birnin London
Wani Jirgin Jami'an tsaro da ke shawagi a birnin London REUTERS/Luke MacGregor
Talla

Ana sa ran shugabannin kasashe 120 za su halarci taron bude wasannin. Wadanda suka hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firmainitan Japan Yoshihiko Noda.

Sarauniya Elizabeth ce zata bude bukin, inda kuma fitattun mawaka a duniya za su cashe.

Rahotanni sun ce uwar gida Michelle Obama ita ce zata jagoranci tawagar Amurka, kamar yadda aka ruwaito yana da wahala Obama ya samu damar kai ziyara a London.

Sai dai kuma akwai shugabannin da sai dai su kalli wasannin ta kafar Telebijin saboda takunkumin tafiye tafiye da aka kakaba masu, shugabannin kuma sun hada da Bashar Assad na Syria da Robert Mugabe na Zimbabwe da Al Bashir na Sudan sai kuma Lukashenko na Belarus.

Amma babu wani tabbaci ko Mahmoud Ahmadinejad na Iran zai kai ziyara birnin na London.

Akwai tsoffin ‘yan wasa da za’a karrama a bukin bude wasannin, kamar fitattcen dan damben Boxing din duniya Muhammed Ali.

Za’a dai gudanar da wasannin Olympic ne a biranen Cardiff da Coventry da Glasgow da Manchester da kuma Newcastle.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.