Isa ga babban shafi
Olympics

Senegal ta samu hurumin shiga Olympics bayan doke Oman

Kasar Senegal zata kai ziyara London a wasannin kwallon kafa na Olympics bayan doke Oman ci 2-1. Kasashe 16 ne zasu buga wasan kwallon kafa a Olympics, kuma yanzu Afrika tana da wakilcin kasashe hudu, da suka kunshi Gabon da Morocco da Masar da kuma Senegal yanzu da ta samu hurunin karshe.

'Yan wasan kwallon kafar kasar Senegal a lokacin da suke murnar lashe wasan zuwa Olympics a Birnin London
'Yan wasan kwallon kafar kasar Senegal a lokacin da suke murnar lashe wasan zuwa Olympics a Birnin London REUTERS/Darren Staples
Talla

Yanzu haka Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta ware Spain da Brazil da Mexico da Ingila da zata dauki nauyin wasannin, a matsayin manyan kasashen da baza su kara da juna ba a zagayen farko.

Ingila a karon farko zata haska a Olympics tun shekaru 50 da suka gabata, ita ce kasar da zata jagoranci rukunin A.

Kasar Mexico kuma ita ce kasar da zata jagoranci rukunin B.

Brazil kuma ita ce zata jagoranci rukunin C sai Spain da aka ware domin jagorantar rukunin D.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.