Isa ga babban shafi
Wasanni

Nadal da sharapova sun lashe Roland Garros

Wallafawa ranar:

Rafael Nadal na Spain da Maria Sharapova ta rasha su ne suka lashe kofin Roland Garros, gasar French Open da ake gudanarwa a Faransa a bana. Nadal ya lashe kofin ne karo na Bakwai bayan ya lallasa a Novak Djokovic a wasan karshe da aka kwashe kwana biyu ana gudanarwa. Maria sharapova kuma ta lashe kofin ne karo na Farko bayan ta lashe kofunan gasar Wimbledon, US Open da Australian Open a bana.

Filin wasan Roland Garros a Faransa
Filin wasan Roland Garros a Faransa
Talla

Nadal shi ne mutum na farko da ya lashe kofin gasar sau Bakwai.

Novak Djokovic dai a bana ya yi fatar lashe grand slams ne guda hudu bayan ya lashe Wimbledon, US Open da Australian Open

Ruwan sama da aka tabka a birnin Paris a ranar Lahadi shi ne ya kawo tsaikun kammala wasan karshe a fafatawar Novak Djokovic da Rafel Nadal, inda aka dage wasan zuwa ranar Litinin.

Novak Djokovic dai shi ne na daya a duniya kuma Rafeal Nadal ne ke bi masa a matsayin na biyu.

Sai dai Djokovic bai taba samun galabar Nadal ba a Rolanda Garros amma ya lallasa Nadal sau uku a wasu wasannin karshe da suka fafata.

Djokovic ne dai ya yi waje da Roger Federer a wasan kusa da karshe, kuma ya rama kashin da ya sha ne hannun Ferderer a bara.

A ranar Assabar ne a karon Farko Maria Sharapova ‘Yar kasar Rasha ta lashe kofin gasar Rolland Garros ta French Open da ake gudanarwa a kasar Faransa bayan ta doke Sara Errani ta Italiya.

Sharapova dai yanzu ta shiga sahun mata 10 suka lashe Roland Garros bayan ta lashe kofin Wimbledon da Us Open da Australian Open.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.