Shugaban Gudanarwar kungiyar kasashen Afrika ta AU, Jean Ping, yace al’amurra sun daidaita a kasar Guinea Bissau, kwanaki biyu bayan barazanar juyin mulkin da aka samu.Dangane da wannan batu ne Muhammad Salisu Hamisu ya tattauna Dr. maina Bukar na Jami’ar Abdulmuni a Nijar.
Yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai kasar, Ping yace, tattaunawar da ya yi da bangarori da dama a kasar, sun tabbatar masa da cewa, harkoki sun koma kamar yadda suke a da, inda ya bukaci ‘Yan siyasar kasar da fararen hula da soji da hukumomi daukar matakin sasantawa da juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu