Kalubalen da 'yan jarida ke fuskanta yayin gudanar da aikinsu
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:00
Shirin Rayuwata a wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kan irin kalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu, musamman batun cin zarafi da suke fuskanta daga jami'an tsaro.Yan jaridar da ake ciwa zarafi dai sun hada da Maza da Mata, wadanda a wasu lokutan kan samu raunuka har ma da rasa rai.
Na baya bayan nan shine batun kama ‘yar jarida Samira Sabou a Jamhuriyar Nijar da hukumomin kasar suka yi bisa zarginta da aikata laifin wallafa labaran da ke iya tayar da hankulan jama’a da kuma taimaka wa wata babar kasar waje. Wadda a ranar laraba da ta gabata mhukuntan Jamhuriyar Nijar din suka bada belinta.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Zainab Ibrahim....
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu