Shirin 'Dandalin Nishadi' na wanna mako ya kawo muku batutuwa da dama da suka shafi nisadi da nishadantarwa, kama daga labaran kamfanin fina finan Kannywood na Najeriya da ma labarin mawakin Najeriya, Davido wanda kwatsam wata mata ta fito tana zarginsa da yi mata juna biyu. Shirin ya mayar da hankali ga sanarwar murabbus wanda shahararren mawakinn salon Pop, dan Birtaniya, Elton John ya yi. Elton John ya shafe shekaru da dama yana nishadantarwa, kuma ya samu nasarori da dama a sana'ar tasa.
Sauran kashi-kashi
-
Dambarwar da ta biyo bayan taron mawaka da aka sani da Met Gala
A cikin shirin Dandalin Nishadi,za mu ji a ina ka kwana biyo bayan taron mawaka na Duniya da aka sani da Met Gala,banda haka wasu daga cikin labaran da suka hada da taron masu shirya fina-finai a birnin Cannes na Faransa na daga cikin wasu labaran da za a ji a cikin wannan shiri daga Rfi.19/05/202420:00 -
An sace kyautar Carosse d’Or a gidan mai shirya fina-finai Souleymane Cisse
Shekara daya kenan da fittacen mai shirya fina-finan kasar Mali darekta Souleymane Cissé ya karbi kyautar Carrosse d'Or, karramawa da aka bashi a birnin Cannes na kasar Faransa lokacin bikin baje kolli da karama masu shirya fina-finan Duniya.Darekta Souleymane Cissé na daga cikin ziratan masu shirya fina-fina a Afrika,wanda tsawon shekaru 50 ya kasance mai fada a ji a wannan masana’anta.04/05/202419:24 -
Aya Nakamura,da Gazo suka lashe kyautar mawakan shekara na Faransa
An gudanar da bikin bayar da kyaututuka ga mawakan zamani a birnin Paris na kasar Faransa, inda mawaka da suka yi fice kamar su Aya Daniocko da aka fi sani da sunan Aya Nakamura, da Ibrahim Diakite mai suna Gazo suka kasance a sahun gaba a wannan biki na mawaka a Faransa.27/04/202419:34 -
Ƙorafin Zango ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen Kannywood
Shirin 'Dandalin Nishaɗi' na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya maida hankali kan wani batu da ya kare da shafukan sada zamunta wato kalaman da ɗay daga cikin jarumai a masana’antar fina-finai ta Kannywood Adam A Zango ya yi wanda ya fito tare da bayyana damuwa kan abin da ya kira butulci da aka masa, al’amarin da ya janyo martani daga da damacikin masu bibiyar masana’antar ta Kannywood. Sai kuma yadda ake shirin bikin kalankuwa na Femua da zai gudana a kasar Cote d’Ivoire.20/04/202420:12 -
Bangaren masana'antu zasu iya taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya
Wannan bikin baje kolin fasaha karkashin inuwar Bankin Afirka, a karkashin sa ido da gudanarwa masana’anta da kuma wurin koyon ayuka na Soto Gallery ya shirya, yana baiwa matasa masu hazaka da fasaha damar samun horo na zamani da ya dace daga kowace kusurwa ta Najeriya.23/03/202420:10