Shirin Dandalin Nishadi tare da Hauwa Kabir na wannan makon ya tattauna ne tare da jarimar fina-finan Kannywood, wato Jamila Nagudu.
Jarumar ta yi wa Hauwa Kabir bayani kan abubuwan da suka shafi rayuwarta ciki kuwa har da batun aure, inda ta ce, tana matukar burin ganin ta a dakin mijinta.
Kazalika ta bayyana irin jerin kalubalen da Kannywood ke fuskanta, inda ta ce sana'arsu a yanzu tana fuskantaar baranazar durkushewa saboda fina-finan India da ake fassarawa a harshen Hausa.
Kazalika shirin ya zanta da wani shahararren mawakin Hausa.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu