Dr. Rahmatu Hassan kan ceto kananan yara da ke fama da karancin abinci a Duniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:30
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta ceto kananan yara miliyan 30 da ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, ko kuma tamowa a sassan duniya, tana mai gargadin cewa, miliyan 8 daga cikinsu ka iya mutuwa nan kusa.
Daga cikin kasashen da ke fama da wannan matsalar har da Najeriya da Nijar da Chadi da Mali da Kenya da Sudan da Somalia da Yemen da Afghanistan da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.
A game da wannan batu, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Dr. Rahmatu Hassan, kwararriyar likita a birnin Abuja.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu