Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kano za ta tilasta gwajin jini kafin aure don dakile yaduwar cutuka

Rahotanni daga jihar Kano ta arewacin Najeriya na nuna yiwuwar gwamnati ta gabatar da wata doka da za ta tilastawa jama'a gwaji kafin aure a wani yunkuri na dakile yaduwar cutuka musamman wadanda akan gajesu ta nau'in jini ciki har da amosanin jini ko kuma sickle cell.

Matukar gwamnati ta sahale wannan kudiri zuwa doka, masana na ganin hakan zai taimaka wajen rage yawan cutukan da ake samu sanadiyyar auratayya da ma wadanda yara ke gada daga iyaye.
Matukar gwamnati ta sahale wannan kudiri zuwa doka, masana na ganin hakan zai taimaka wajen rage yawan cutukan da ake samu sanadiyyar auratayya da ma wadanda yara ke gada daga iyaye. ALFREDO ESTRELLA / AFP
Talla

Wasu majiyoyi kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito sun ce yanzu haka Majalisar dokokin jihar ta yiwa wani kudirin doka karatu na biyu a kokarin tilasta daukar wannan mataki na gwaji kafin aure.

Majiyoyin sun ce tun da fari dan majalisar jihar mai wakiltar Takai Musa Ali Kachako ne ya gabatar da kudirin da ke neman tilastawa masoyan yin gwajin don rage yawan masu fama da cutar ta amosanin jinin wadanda jihar ke ganin karuwarsu.

Tun gabanin fara zama kan wannan doka dai akwai tanadin gudanar da gwajin kafin aure wanda a wasu lokutan waliyyai kan ki amincewa da daura aure har sai an mika takardun gwajin don kaucewa hada auren da ke da matsala musamman ta fuskar lafiya.

Matukar majalisar ta Kano ta amince da wannan kudiri zuwa doka kuma ya samu sa hannun gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf kai tsaye za a rage yawan cutukan da ake samu sanadiyyar auratayya ba tare da gwaji ba.

Masana lafiya a jihar ta Kano sun shafe tsawon shekaru suna kiraye-kirayen ganin mahukunta sun dauki matakin tilasta irin wannan gwaji a kokarin dakile cutukan da sabawar nau'in jini kan haddasu, ko kuma cutuka na kai tsaye da kan shafi rayuwar ma'auratan ko ma wadanda yaran da za a haifa ka iya gado.

Cutar sikila na sahun cutukan da 'ya'yan kan yi gado daga jikin iyayen da ke da wasu nau'in jini. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.