Yadda ake gane alamomin cutar da ke kashe mutane a Kano
Mahukunta a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da fadakar da jama’a game da alamomin wata nau’in cuta mai saurin kisa da yanzu haka ta bulla a wasu sassan Jihar. Daga cikin alamomin wannan cuta har da zubar majina daga hanci da tari babu kakkautawa da zazzabi da kuma ciwon makoshi.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:18
Ya zuwa yanzu, cutar da ake kiran ta 'diptheria' a harshen Turanci ko kuma mashako a Haussa, ta halaka kusan mutane 30, baya ga wasu da dama da ke kwance a asibiti.
Tuni dai aka bude wuraren killlace wadanda suka kamu da cutar don magance bazuwarta.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Abubakar Isa Dandago daga birnin Kano
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu