Isa ga babban shafi
ZABEN GWAMNA

Kotun daukaka kara ta tabbatar da Uba Sani a matsayin zababben gwamnan Kaduna

Kotun daukaka kara da kee zamanta a Abujan Najeriya, ta tabbatar da Uba Sani, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna da ke Arewacin kasar.

Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani yayin bukin kaddamar da horon sabbin 'yan banga a jihar. 02/09/23
Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani yayin bukin kaddamar da horon sabbin 'yan banga a jihar. 02/09/23 © Sen. Uba Sani X handle
Talla

Kotun mai alkalai uku, ta yi watsi da korafin da dan takarar gwamnan karkashin jam’iyyar PDP, wato Muhammad Ashiru ya shigar gabanta, wanda ta ce bashi da cikakkun hujjoji.

Kotun ta kuma amince da hujjojin da gwamna Uba Sani ya gabatar mata kan zaben da aka gudanar.

Ashiru dai ya daukaka kara zuwa kotun ne, bayan hukuncin da kotun sauraron kararrain zabe ta yanke, wadda ta tabbatar da nasarar da gwamna Uba Sani ya samu na zaben da ya gabata.

Jam’iyyar APC ce kan gaba a zaben da yawan kuri’u 730,002, inda ya PDP, ta samu kuri’u719,196, wanda hakan ya sanya hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEc ta ayyana Uba Sani a matsayin wandda ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.