Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kaduna ta kulle makarantar Al-Azhar saboda mutuwar dalibi

Gwamnatin Jihar Kaduna a Najeriya ta bada umarnin kulle makarantar Al-Azhar da ke Zaria biyo bayan mutuwar wani dalibi da ake zargin duka ne yayi ajalin sa.

Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani © Sen. Uba Sani X handle
Talla

Bayanai sun nuna cewa Marwan Nuhu Sambo ya rasa ransa ne bayan duka da ake zargin shugaban makarantar da mataimakin sa sun hada gwiwa wajen yi masa, saboda laifin kin zuwa makaranta.

Tuni dai jami’an tsaro suka chafke shugaban makarantar da wasu daga cikin malamai da ake zargin su da hannu a aikata wannan laifi.

Ta cikin wata takarda da hukumar da ke sanya idanu kan makarantu ta jihar ta fitar, ta ce an rufe makarantar har zuwa lokacin da sakamakon likitoci zai fito kan hakikanin abinda ya yi ajalin matashin Marwan.

Tuni dai gwamnatin jihar karkashin Gwamna Uba Sani ta ce zata jajirce wajen ganin an gudanar da bincike tare da hukunta wadanda aka samu da laifi da kuma barin doka ta yi aikin ta.

Sanarwar gwamnatin ta bukaci jama’a su kwantar da hankalin su tare da gujewa daukar doka a hannun su, sannan su bar maukunta su yi aikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.