Isa ga babban shafi

Yajin aiki: Likitocin Najeriya sun shirya gudanar da zanga-zanga a kowacce rana

Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta ayyana gudanar da zanga-zanga a fadin kasar na kowacce rana tare da zaburar da cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya.

Kungiyar likitocin kasar na zargin gwamnatin da gazawa wajen
Kungiyar likitocin kasar na zargin gwamnatin da gazawa wajen © dailytrust
Talla

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, kungiyar da a halin yanzu take yajin aiki a fadin kasar ta ce za a fara zanga-zangar ne a ranar Laraba 9 ga watan Agusta da karfe 10:00 na safe.

Sanarwar wadda aka fitar, bayan kammala taron majalisar zartaswar kungiyar ta NERD, ta ce bata da zabi face fara zanga-zangar, yayin da ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani a fadin kasar.

Kungiyar ta ce lokaci ya yi da duniya za ta ga yadda tabarbarewar almundahana da cin hanci da rashawa a bangaren kiwon lafiya da ke kamari, wanda a tsawon wadannan shekaru shine yake haifar da tafiya yajin aikin da likitoci ke yi.

A makon jiya ne, gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar cewa, za ta yi amfani da tsarin idan babu aiki, to kuwa babu biya ga likitocin da suka shiga yajin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.