Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Wani abu da ake zato bam ne ya tashi a Kaduna

A Najeriya, mazauna unguwar Hayin dan Mani ta karamar hukumar Igabi a  jihar Kaduna, sun fada cikin fargaba biyo bayan fashewar wani abu da ake zato bam ne a daren Juma’a.

Taswirar Naqjeriya dake nuna jihar  Kaduna.
Taswirar Naqjeriya dake nuna jihar Kaduna. AFP
Talla

Lamarin ya auku ne a kusa da shagon wani mai na’urar hada hadar kudi ta P.O.S, kusa da masallacin Abubakar Sadiq, a cewar wasu mazauna unguwar.

Jardar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a kasar ta ruwaito cewa an gano  wani abu da ake zato bam ne  a kusa da wani babur da aka ce mallakin mai hada hada da P.O.S.

Wani dan aikin sa ki a unguwa, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce fashewar ta raunata mai shagon P.OS din, wanda aka garzaya da shi asibiti tare da saura mutane 6 ad suka samu rauni, saboda yadda  yadda raunukan kafafunsa da yatsunsa suka tsananta.

Gwamnatin jihar da kuma rundunar ‘yan sandan jihar ba su ce uffan a kan wannan lamari ba.

Wannan fashewar na zuwa ne ‘ya makonni bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro  Samuel Aruwan ta gargadi mazauna jihar da su yi taka tsantsan saboda akwai rahotannin da ke cewa ‘yan ta’adda na shirin dasa bama bamai a makarantu, kasuwanni da wuraren ibada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.