Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Hare-haren 'yan bindiga sun kashe mutane 101 cikin mako guda a Najeriya

Akalla mutane 101 suka mutu a Najeriya cikin mako guda sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da sauran tashe-tashen hankula wanda ke matsayin alkaluma mafi yawa da kasar ta gani cikin makwanni 8 a jere.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Alkaluman da jaridar Premium Times ta wallafa ya nuna yadda aka samu karuwar kasha 200 idan aka kwatanta da alkaluman makon jiya da aka samu rasa rayukan mutane 32 sakamakon hare-haren.

Cikin mutanen 101 har da basaraken gargajiya da ‘yan bindiga suka kashe a Kaduna kana manoma 45 a Nasarawa sai kuma wasu mutum 38 da ‘yan bindiga suka kashe a Kaduna.

Alkaluman na Premium Times ya nuna cewa mabanbantan hare-hare 8 ne ya kai ga kashe mutanen 101 a shiyyoyin arewa 3 dukkaninsu.

A wasu mabanbantan hare-hare a Zamfara, ‘yan bindigar sun kashe mutane 2 tare da kora tarin dabbobi a Tungar Bai yayinda suka kashe wasu mutum 7 a Katsina baya gas ace wasu da dama.

Can a karamar hukumar Giwa ‘yan bindiga sun harbe wani Magaji Ibrahim har lahira sa’o’I kalilan bayan sun kashe mutane 38.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.