Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna-'yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutum guda suka kuma kwashe mutane a coci

An kashe akalla mutum guda a wani hare da wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne suka majami’ar Haske Baptist Church da ke kauyen Manini Tasha a  karamar hukuma Chikun  ta jihar Kaduna, Najeriya.

Misalin 'yan bindiga da ke addabar al'umma a sassan Najeriya.
Misalin 'yan bindiga da ke addabar al'umma a sassan Najeriya. New Indian Express
Talla

Ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani a hukumance a game da lamarin, amma rahotanni daga yankin na cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu masu ibada, yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

Majiyoyi sun ce wanda aka kashen, wani likita ne da ke aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar kaduna din.

Yankin karamar Chukun din dai yan fama da radadin ayyukan ‘yan bindiga, kuma har yanzu ba a kai ga samun yadda ake so ba duk da  kokarin hukumomi na kare al’umma.

 A ranar Juma’a, an tsinci gawarwakin wasu dalibai 3 daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka sace a jami’ar Greenfield da ke karamar hukumar Chukun din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.