Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

Ƴan bindiga sun kai hari wani asibiti tare da sace ma'aikatan jinya a Kaduna

Wasu Ƴan bindiga a Jihar Kaduna dake Najeriya sun kutsa kai wani asibiti dake karamar hukumar Kajuru inda suka kwashe masu aikin taimakawa likita guda biyu.

Jami'an tsaron Najeriya a makarantar da 'yan bindiga sukayi garkuwa da dilibai a jihar Laduna
Jami'an tsaron Najeriya a makarantar da 'yan bindiga sukayi garkuwa da dilibai a jihar Laduna Bosan Yakusak AFP/File
Talla

Rahotanni sun ce Yan bindigar sun kai harin ne daren jiya a asibitin dake kula da garuruwan Idon da Makyali da Idon Gida da Kajuru da maro da Kasuwan Magani da Kufana da Kallah da Kurmin Idon da Buda da kuma Afogo.

Jihar Kaduna na cigaba da fuskantar matsalar sace mutane ana garkuwa da su domin karbar diyya.

Ko a jiya mun kawo muku rahotan yadda Ƴan bindigar suka kai hari wata Jami’a mai zaman kanta ta Greens Field inda suka kwashe wasu daga cikin daliban ta bayan kashe ma’aikaci guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.