Isa ga babban shafi

An sace ma'aikatan jirgin ruwa a gabar tekun Najeriya

‘Yan fashi a kan teku, sun kai hari kan wani jirgin ruwan dakon kaya tare da yin garkuwa da ma’aikatansa biyu a gabar tekun Najeriya.

Masu fashin teku a gabar ruwan Najeriya
Masu fashin teku a gabar ruwan Najeriya PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Jirgin wanda aka bayyana cewa na kasar Netherlands ne, an kai masa hari ne a lokacin da ya doshin tashar ruwan birnin Lagos a ranar Talata, kamar dai yadda mai magana da yawun kamfanin Seatrade, wanda ya mallaki jirgin wato Cor Rading ya shaida wa manema labarai.

Kakakin kamfanin yace, ya zuwa jiya, babu wanda ya tuntube su daga wadanda ke rike da ma’aikatansu, ba tare da karin haske kan asalin kasashen su ba.

Yanzu haka jirgin ruwan ya isa tashar ruwan na Lagas da kaya tan 4,800 da kuma sauran ma’aikta 16 dake cikin koshin lafiya, bisa rakiyar jami’an sojin ruwan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.