Biden ya kira Netanyahu ta waya don duba hanyar kubutar da mutanen da Hamas ke tsare da su
Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho a yau Lahadi, inda ya sake duba tattaunawar da ake yi na kubutar da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin da suka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba,sanarwa daga fadar shugaban Amurka.
Wallafawa ranar:
Amurka da Isra’ila na nazari da sa ran lallubo hanyoyin sako mutanen da aka yi garkuwa da su tare da tsagaita bude wuta nan take a Gaza, in ji sanarwar fadar White House, yayin da kokarin diflomasiya ke kara kaimi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da aka dade ana nema a yankin da yaki ya daidaita.
Gwamnatin Isra'ila ta fuskanci matsananciyar matsin lamba daga kawayenta na duniya kan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma masu zanga-zanga a cikin Isra'ila da ke neman a sako mutanen da kungiyar Hamas.
Masar da Qatar da kuma Amurka sun shafe watanni suna kokarin shiga tsakani a wata sabuwar sulhu.
Biden da Netanyahu "sun kuma tattauna batun karuwar isar da agajin jin kai zuwa Gaza ciki har da shirye-shiryen bude sabbin mashigar arewacin kasar daga wannan makon," in ji sanarwar.
"Shugaban ya jaddada bukatar ci gaba da dorewar wannan ci gaban da kuma inganta shi cikin cikakken hadin kai da kungiyoyin agaji," in ji ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu