Isa ga babban shafi

Faransa za ta sanya sojojin ruwanta cikin masu aikin bada agaji a Gaza

Gwamnatin Faransa ta sanar da aike wa da wani jirgin sojojin ruwa yankin Gaza don su sanya hannu a aikin bayar da agaji da ake yi, dai-dai lokacin da Tel-Aviv ke ci gaba da barin wuta ba kakkautawa.

Shugaban Faransa Emmanule Macron da takwaran sa na Masar Abdulfatah Al-sisi
Shugaban Faransa Emmanule Macron da takwaran sa na Masar Abdulfatah Al-sisi REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaban kasar Emmanuel Macron wanda ke sanar da wannan shirin yace jirgin zai bar yankin Toulon cikin sa’o’i 48 masu zuwa kuma aikin sa kawai shine baiwa jama’ar Gaza agajin gaggawa musamman a cibiyoyin lafiya.

Macron wanda ke bayyana wannan mataki yayin taron da ya halarta a birnin Cairo, ya ce zai kuma sake aikewa da jirgin sama makare da kayan agaji masu muhimmanci zuwa yankin Falasdinu duk a kokarin da kasar ke yi na bayar da nata taimako.

Ko da yake nasa jawabi shugaban kasar Masar Abdulfatah Al-sisi ya ce akwai bukatar duniya ta dakatar da shirin Isra’ila na kusatwa Gaza ta kasa cikin gaggawa la’akari da hadarin da ahakn ke da shi.

Al-sisi yace wannan shiri ba zai haifar da da mai ido ba hatta ga ita Isra’ila, abinda zai haifar kawai shine karin mutuwar fararen hula, da kuma jefa gabas da tsakiya cikin hadarin afkawa yaki.

Har yanzu dai babu wata kasa ko kuma hukuma ce da ta bukaci Isra’ila ta tsagaita wuta, ko kuma sanya mata takunkumi kamar yadda aka gani a wasu kasashe, illa dai bukatar ta yi nazari matuka kafin yanke hukuncin kutsawa Gaza ta kasa.

Tuni dai Isra’ilan ta gudanar da wani atisayen sojoji a ci gaba da shirin da ta ke yi na shiga Zirin Gaza ta kasa a kokarin da ta ke yi na shafe Hamas daga doron duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.