Isa ga babban shafi

Iran ta zartas da hukuncin kisa kan mutane 834 cikin shekara 1- Rahoto

Wani rahoto ya nuna yadda mahukuntan Iran suka zartas da hukuncin kisa kan mutanen da yawansu ya kai 834 a shekarar da ta gabata kadai, adadin da ke matsayin mafi yawa da kasar ke kashewa duk shekara tun daga 2015 zuwa yanzu.

Shekarar 2023 ke matsayin lokacin da Iran ta fi yawan zartas da hukuncin kisa a tarihin baya-bayan nan.
Shekarar 2023 ke matsayin lokacin da Iran ta fi yawan zartas da hukuncin kisa a tarihin baya-bayan nan. ASSOCIATED PRESS - STR
Talla

Rahoton wanda na hadaka ne tsakanin kungiyar kare hakkin dan adam ta Iran da ke Norway da kuma takwararta ta Faransa, ya ce tun bayan da mahukuntan Tehran suka kashe mutane 972 a 2015 basu kara zartas da makamancin hukuncin kisan kan mutane masu yawa ba sai a bara inda kasar mai amfani da dokokin addinin Islama ta kashe mutanen 834.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam din biyu sun zargi mahukuntan na Iran da zafafa zartas da hukuncin kisa don firgita jama’a musamman wadanda ke zanga-zangar kisan matashiya Mahsa Amini da ya haddasa kakkarfan bore a sassan kasar cikin shekarar 2022.

Rahoton kungiyoyin biyu ya ce amfani da salon hukuncin kisan shi ke matsayin hanya daya tilo da mahukuntan na Iran ke amfani da shi don ci gaba da rike madafun iko sakamakon kange duk wata barazana daga masu adawa da salon kamun ludayin mahukuntan.

Rahoton ya ce Iran ta kashe mutane 9 masu hannu a kisan jami’in tsaro yayin zanga-zangar 2022 sai wasu 2 a 2022 kana 6 a 2023 sai kuma wani guda a 2024.

A cewar rahoton Iran ta zafafa kashe-kashe a batutuwa masu alaka da ta’ammali da miyagun kwayoyi inda ta kashe mutane 471 a wannan bangare kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.