Isa ga babban shafi

Kasashe 83 na gudanar da taron kawo karshen yakin Rasha da Ukraine

Kasashe fiye da 80 sun gudanar da taro a jiya Lahadi, inda suka tattauna akan matakan da za a bi wajen kawo karshen yakin Rasha da Ukraine. Ko da ya ke kasar Switzerland da ke karbar bakoncin taron ta ce, basu kai ga cimma matakin neman fara tattauna da shugaban Rasha Vladimir Putin kai tsaye ba. 

Taron tattaunawa a kokarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.
Taron tattaunawa a kokarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine. via REUTERS - POOL
Talla

Masu bayar da shawara kan harkokin tsaro na gwamnatocin kasashe 83 ne suka gudanar da taron, wanda kuma shi ne karo na hudu da suke irin wannan haduwa domin nazartar kudurori 10, da shugaba Volodymyr Zelensky ya gabatar kan shirin tattaunawar sulhun maido da zaman lafiyar Ukraine, wadda zuwa yanzu kusan shekaru biyu kenan da Rasha ta kaddamar da yaki kanta. 

Taron na ranar Lahadi dai ya gudana ne a karkashin jagorancin mataimaki na musamman ga shugaban Ukraine, Andriy Yermak da kuma ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis. 

Manyan jami’an sun shaidawa taron manema labarai cewa ya zama dole su gaggauta cimma matsaya kan matakai ko shawarwarin da za a bi wajen kawo karshen yakin Ukraine, sai dai basu kai ga matakin da za su tuntunbi Rasha kai tsaye ba. 

Kafin taron na jiya dai, sau uku manyan jami’an da ke bayar da shawara kan harkokin tsaron kasashe 83 suka gana a Denmark cikin watan Yuni, da Saudiya a watan Agusta da kuma taronsu na Malta a Oktoban shekarar 2023. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.