Isa ga babban shafi

Houthi da Hezbollah sun sake kai hare-hare kan Isra'ila

‘Yan tawayen Houthi na Yemen sun dauki alhakin hari da jirgi marar matuki a Isra’ila da kuma farmaki kan wani jirgin ruwan dakon kaya jiya Talata a tekun Red Sea a wani yunkuri na nuna goyon baya ga Falasdinawa, dai dai lokacin da Isra’ila ke cewa zai dauki tsawon lokaci ta na ci gaba da kai hare-hare a sassan yankin Gaza.

Wani hari da Hezbolla ta kai iyakar Isra'ila.
Wani hari da Hezbolla ta kai iyakar Isra'ila. © JALAA MAREY / AFP
Talla

Jim kadan bayan jawabin babban hafson Sojin Isra’ila Herzi Halevi game da hare-harensu a Gaza ne, ‘yan tawayen Houthi na Yemen suka sanar da farmakar jirgin a tekun Red Sea ta hanyar harba masa makami mai linzami baya ga kai hari da jirage marasa matuka cikin Isra’ila, wanda ke matsayin karon farko da suka iya isar da hari cikin kasar Yahudawan tun bayan faro yakin a ranar 7 ga watan Oktoba.

Isra'ila na ci gaba da kisan kare dangi a Gaza.
Isra'ila na ci gaba da kisan kare dangi a Gaza. AP - Fatima Shbair

Sanarwar da Houthi ta fitar ta ce za ta ci gaba da farmakar Isra’ila da duk wani jirgi da ya nufi kasar matukar ya ratsa Red Sea, dai dai lokacin da alkaluman Falasdinawan da Isra’ila ta kashe ke tasamma dubu 20 galibinsu mata da kananan yara.

A bangare guda wasu Sojin Isra’ila 9 sun jikkata a harin da mayakan Hezbolla daga Lebanon suka kai kan iyakar kasashen biyu yayinda martinin Isra’ila ya kashe fararen hula 2 a kudancin Lebanon.

Bangarorin biyu na Hezbollah da Houthi na ci gaba da kai hare-hare don tilasta Isra’ila dakatar da kisan kare dangin da ta ke yi wa Falasdinawa a Gaza, sai dai Halevi a jawabin kai tsaye ta gidan talabijin din Isra’ila ya ce sojojin Yahudawan za su tsawon watanni a nan gaba suna ci gaba da kai hare-hare kan Falasdinawa.

A cewarsa dole su kakkabe 'yan ta'addan da ke yankin, ta yadda yanzu haka sun bankado maboyarsu fiye da 100 tare da kame da dama, batun da Hamas ke ci gaba da musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.