Isa ga babban shafi

RSF ta maka Isra'ila gaban kotun ICC kan kashe 'Yan Jarida a Gaza

Kungiyar kare ‘yan Jarida ta Duniya wato RSF a takaice, ta sake shigar da kara gaban kotun duniya ICC, dangane da laifukan yakin da ta ce sojojin Isra'ila sun aikata na kashe Falasdinawa a ‘yan Jarida a Zirin Gaza.

Wasu 'yan Jarida a yankin Falasdinawa na gabar Yamma da kogin Jordan, yayin tattaki zuwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya don gudanar da zanga-zangar lumana.
Wasu 'yan Jarida a yankin Falasdinawa na gabar Yamma da kogin Jordan, yayin tattaki zuwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya don gudanar da zanga-zangar lumana. © Nasser Nasser/Associated Press
Talla

Koken na baya bayan nan da kungiyar ta RSF da ke da hedikwata a birnin Paris ta shigar a ranar Juma'a, ya bukaci kotun duniyar ta gudanar da bincike kan mutuwar Falasdinawa ‘yan jarida guda bakwai a baya bayan nan, wadanda Isra’ila ta kashe a Gaza daga ranar 22 ga Oktoba zuwa 15 ga watan Disamba.

Daga cikin ‘yan cikin ‘yan jaidar da aka kashe akwai wakilin kafar watsa labarai ta Al Jazeera da ke aikin daukar mata hotuna, wato Sameer Abudaqa, wanda dakarun Isra’ila suka kashe a makon jiya.

A ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata, kungiyar kare ‘yan jaridun ta duniya ta shigar da korafi na farko gaban kotun ICC akan mutuwar ‘yan jarida da dama, wadanda tace adadinsu jimilla ya kai 66, tun bayan barkewar yaki tsakanin isra’ila da Hamas a Gaza.

Ya zuwa yanzu dai Falasdinawa sama da dubu 20,000 dakarun Isra’ila suka kashe a Zirin na Gaza, tun bayan kaddamar da hare-haren ramuwar gayyar da suka yi daga ranar 7 ga watan Oktoba, bayan farmakin da mayakan Hamas suka kai tare da kashe Yahudawa akalla dubu 1 da 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.