Isa ga babban shafi

Ya kamata a kawo karshen cin zalin da ake yiwa nahiyar Afirka - MDD

Majalisar Dinkin Duniya tare da Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, sun cimma yarjejeniyar samar da wani shiri na musamman da zai rika kare hakkokin dan adam a nahiyar Afirka, tare da kara kaimi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, hadi da kawo karshen zaluncin da nahiyar ke fuskanta.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya daga hagu, António Guterres, tare da shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya daga hagu, António Guterres, tare da shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat. © UN
Talla

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, da kuma shugaban kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, sun sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne a birnin New York na kasar Amurka.

António Guterres y ace, Afirka na bukatar a rika yi mata adalci a dukkanin matakai na kasa da kasa, domin ta jima ta fama da zalunci ta a huldudodi da dama daga kasashen ketare shekaru da dama.

Babban magatakardar ya buga misali da zalunci na farko da nahiyar ta fuskanta, a lokacin mulkin mallakar turawan yamma, abin da ya kai har aka rika mayar da su bayi, kuma wannan rashin adalci har yanzu yana ci gaba da wanzuwa amma a zamanance.

Ko da yake a taron ganawar da suka, Moussa Faki ya kawo batun zaman lafiya da kuma rashin tsaron da nahiyar ke fama da shi, musamman batun ayyukan ta’addanci, wanda shi ke haifar da koma baya ga Afirka.

Faki ya bayyana cewa, Afirka na fama da matsalar tattalin arziki, abin da y ace ya rubanya sakamakon annobar Covid-19, matsalar sauyin yanayi, da kuma rikicin Ukraine da Rasha da ya kawo cikas ga bangaren samar da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.