Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta bada sammacin kama shugaban Syria

Faransa ta bada sammacin kasa da kasa domin cafke shugaban Syria Bashar al-Assad bisa zargin sa da hannu wajen aikata laifukan cin zarafin bil’adama ta hanyar kaddamar da harin makami mai guba a shekarar 2013.

Shugaban Syria Bashat Al-Assad
Shugaban Syria Bashat Al-Assad © REUTERS/SANA
Talla

Wata majiyar shari’a ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, har ila yau ana zargin shugaba Assad da hannu wajen aikata laifukan yaki ta hanyar kaddamar da harin makami mai guba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 1 da 400 a kusa da birnin Damascus a cikin watan Agustan 2013.

Kazalika an bayar da sammacin kasa da kasa na kama dan uwan shugaba Assad mai suna Maher da ke jagorantar wani sashi na manyan sojojin Syria da kuma wasu manyan janar-janar na soji biyu da su ma aka bada sammacin a kansu.

Tun shekara ta 2021, kotun birnin Paris na Faransa wadda ta damu da laifukan yakin da aka aikata, ta fara gudanar da bincike ka harin na makami mai guba.

Yadda aka rika ceto mutanen da suka shaki gubar da ake zargin gwamnatin Syria ta Bashar al-Assad da harbawa.
Yadda aka rika ceto mutanen da suka shaki gubar da ake zargin gwamnatin Syria ta Bashar al-Assad da harbawa. AFP

Kotun ta kaddamar da binciken ne bayan wasu kungiyoyi masu zaman Kansu da suka hada da cibiyar da ke sanya ido kan kafafen yada labarai da fadin albarkacin baki ta Syria  da Kungiyar Lauyoyi ta Open Society Justice Initiative da Hukumar da ke sanya ido kan cin zarafin bil’adama ta Syria sun shigar da kara a gabanta.

A wancan lokacin dai, wasu hotunan bidiyo sun nuna yadda harin makamin mai guba ya lakume rayukan hatta kananan yara baya ga wadanda aka nuna suna fitar da kumfa daga bakinsu, inda likitoci suka yi ta kokarin ceto su daga mutuwa ta hanyar shaka musu iskar Oxygen.

Wannan al’amarin ya janyo caccaka daga kasashen duniya da dama, amma shugaba Assad ya musanta hannu a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.