Isa ga babban shafi

Saudiya za ta tallafa wa kasashen Afrika don rage bashin da ke kansu

Ministan Kudin Saudiya Muhammad Al-Jadaan, ya ce asusun raya kasashe na kasar zai kulla yarjejeniya tsakaninsa da kasashen Afirka, wadda a karkashinta Saudiyan za ta tallafa musu da Riyal biliyan 2, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 533. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da Sarkin Saudiya.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da Sarkin Saudiya. © Nigeria presidency
Talla

 

Ministan Kudin ya bayyana haka ne yayin taron karfafa alakar tattalin arziki tsakanin kasashen Larabawa da na Afirka a karkashin jagorancin Saudiya a wannan Alhamis a birnin Riyadh, inda ya kara da cewar yanzu haka gwamnatinsu tare da wasu abokan huldarta na tsara shirin tallafa wa wasu kasashen Afirka ciki har da Ghana, wajen rage musu nauyin bashin kudaden da hukumomin bayar da lamunin kasa da kasa ke bin su. 

A gefe guda kuwa duk dai yayin taron tattalin arzikin,  Ministan Kula da Harkokin Zuba Hannayen Jarin kasar ta Saudiya Khallid Al-Fatlih, ya yi alkawarin cewa asusunsu da ya kunshi sama da dalar Amurka biliyan 700 zai zuba hannayen jari don aiwatar  da manyan ayyukan raya kasa a sassan nahiyar Afirka. 

Ministan Kula da  makamashi na Saudiya kuwa, rattaba hannu ya yi kan yarjejeniyar bunkasa samar da makamashin da kuma hada-hadarsa tsakaninsu da kasashen Najeriya da Senegal, da  Chadi da kuma Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.