Isa ga babban shafi

Majalisa ta bukaci Faransa ta gaggauta inganta alakarta da Afrika

Afirka – ‘Yan majalisar dokokin Faransa sun bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta aiwatar da sauye-sauye domin inganta dangantakarta da kasashen Afirka, lura da yadda kasashen Rasha da China ke fadada karfin fada-a-ji a yankin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Omar Havana
Talla

Wani rahotan majalisar da aka wallafa a Larabar nan mai dauke da shafuka 170 ya biyo bayan damuwar da ake nunawa a Faransa a kan yadda ake samun karuwar kyamar kasar a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.

Rahotan da Bruno Fuchs na jam’iyyar DM da Michele Tabarot na Republican suka jagoranci rubuta shi, ya bayyana cewar kasar Faransa na fuskantar matsaloli wajen tinkarar sauye -sauyen da ake samu a nahiyar Afirka.

Shugaba Emmanuel Macron yayin wani taron G5 Sahel
Shugaba Emmanuel Macron yayin wani taron G5 Sahel Guillaume Horcajuelo/Pool via REUTERS

Rahotan Majalisar ya ce ‘yan Afirka na bukatar sauyi a kan manufofin Faransa, saboda haka ya zama wajibi a samar da shi cikin gaggawa domin magance matsalar da kuma kauce wa rasa yarda daga jama’ar nahiyar.

Shi dai wannan rahoto mai shafuka 170 da aka gabatar da shi, ya biyo bayan hirarraki da ganawar da ‘yan majalisar suka yi da tarin ‘yan siyasar Afirka da Faransa da jami’an soji da wakilan kungiyoyin fararen hula da kuma ‘yan jarida.

Mawallafa rahotan sun ce Faransa ta ki aiwatar da manufofin Afirka masu inganci a kokarin da take yi na sabunta danganta da nahiyar da kuma kauce wa kura-kuran da aka samu a baya, saboda rashin fahimtar yadda Afirka take da kuma rungumar manufofin siyasa marasa inganci.

Kasar Faransa dai ta kawo karshen shirinta na yaki da masu ikrarin jihadi a Mali da Burkina Faso, yayin da a ‘yan kwanakin nan kuma ta fara janye sojojinta 1,400 da ke Jamhuriyar Nijar bayan kifar da gwamnatin shugaba Bazoum Mohammed, daya daga cikin abokan tafiyar kasar.

Shugaba Emmanuel Macron da Mahamat Idriss Deby na Chadi
Shugaba Emmanuel Macron da Mahamat Idriss Deby na Chadi AFP - LUDOVIC MARIN

Sojojin da suka yi juyin mulki a wadannan kasashe guda 3 sun kori tawagar Faransa, yayin da Mali ta kulla yarjejeniyar tsaro da tawagar sojojin hayar Rasha da ake kira Wagner.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha fadin bukatarsa ta yin sauye-sauye masu matukar tasiri a kan manufofin kasar a Afirka, wajen watsi da tsohon shirin ‘Franceafrique’ wanda kasar ke amfani da shi wajen barin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a karkashin kulawarta.

A watan Satumbar da ya gabata, shugaba Macron ya ce ‘Franceafrique’ ta mutu, amma kuma sau tari a kan soki kasar a kan yadda take kwan-gaba kwan-baya a kan yadda take alaka da kasashen na Afirka.

Yayin da Faransar ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar a cikin wannan shekara, kasar ta kuma amince da nadin Mahamat Idriss Deby wanda ya hau karagar mulki ba tare da bin tanade- tanaden kundin tsarin mulki ba a shekarar 2021, bayan kashe mahaifinsa.

Rahotan majalisar ya bukaci sake fasalin manufofin kasar ta yadda zai zaburar da kasashen Afirka su bukaci dangantaka mai inganci a tsakaninsu da Faransar.

Marubuta rahotan majalisar sun ce kawo sauyi a fasalin dangantakar ya zama wajibi, inda suka bukaci fahimta mai kyau daga Faransar tare da kauce wa yin alkawura ba tare da cikawa ba.

Rahotan ya kuma bukaci yin garambawul a kan yadda kasar ke bada agaji ta hanyar da za ta kara yawansa da kuma takaita rancen da take bayarwa, tare da kawo karshen rashin tabbas a kan shirinta na bada biza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.