Isa ga babban shafi

Tunisia na shirin kafa dokar dauri kan duk wanda ya kulla alaka da Isra'ila

‘Yan majalisar Tunisia sun fara muhawara kan kudirin kafa dokar haramta kulla duk wata alaka da Isra’ila, wadda a karkashinta duk wanda aka samu da laifin zai fuskanci hukuncin daurin shekarun da suka kama daga 6 zuwa 10, tare da biyan tarar dinare dubu 10 zuwa dubu 100.

Majalisar dokokin kasar Tunisia.
Majalisar dokokin kasar Tunisia. REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Idan kuma har aka kama mutum da sake aikata laifin na alaka da Isra’ila, to fa yana iya fuskantar hukunci mai tsauri na daurin rai da rai.

Matakin ‘yan majalisar na Tunisia ya zo ne a daidai lokacin da takwarorinsu na Bahrain suka dakatar da duk wata huldar kasuwanci da kuma ta diflomasiya da Isra’ila bayan janye jakadansu daga kasar, biyo bayan kisan fararen hular da sojojin Isra’ilar ke yi a Zirin Gaza da sunan yakin neman murkushe mayakan kungiyar Hamas.

Ya zuwa wannan lokaci dai shugabancin gwamnatin kasar ta Bahrain bai tabbatar da daukar matakin a hukumance ba, yayin da ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce mahukuntan Bahrain din basu sanar da ita batun katse huldar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.