Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki a Gaza kan rikicin Hamas da Isra'ila

Gwamnatin yankin Falasdinu ta ce hare-haren da Isra’ila ta kai cikin daren Lahadi sun hallaka mutane 60, ciki har da wani hari da ta kai wani gida da ke Jabaliya a Arewacin Gaza.

Yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya, bayan wani hari da Isra'ila ta kai Gaza a ranar 23 ga watan Okotan 2023.
Yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya, bayan wani hari da Isra'ila ta kai Gaza a ranar 23 ga watan Okotan 2023. AP - Ariel Schalit
Talla

Gwamnatin ta kuma ce akwai karin wasu mutane 10 da suka sake rasa rayukansu a Litinin din nan.

Sojojin Isra’ila sun ce a cikin daren Lahadi sun yi ruwan bama-bamai a yankin Gaza, inda suka samu nasarar kai hari wasu daga cikin cibiyoyin kungiyar Hamas.

Isar kayan agaji

Izuwa ranar Litinin din nan, manyan motoci dauke da kayan agaji sun sake isa yankin Gaza ta iyakar Rafah da ke kasar Masar, rana ta uku ke nan da ake samun wannan nasarar.

Amurka ta sha alwashin ci gaba da kai kayan agaji yankin na Gaza, bayan da Isra’ila ta datse masa ruwan sha da wutar lantarki dama hana shigar da kayan abinci cikinsa.

Wasu daga cikin manyan motocin da ke dauke da kayan agaji a yankin Gaza.
Wasu daga cikin manyan motocin da ke dauke da kayan agaji a yankin Gaza. © REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

A ranar Asabar motoci 20 dauke da kayan agaji ne suka isa yankin, sai dai a ranar Lahadi an samu raguwarsu zuwa 14.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yankin na Gaza na bukatar akalla motocin kayan abinci dari a kowace rana, don wadata kimanin mutane miliyan biyu da dubu dari 4 da kusan rabinsu hare-haren Isra’ila ya raba da gidajensu.

Halin da ake ciki a kan iyakar Lebanon

Hukumar kulada kauran baki ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kimanin mutane dubu 19 da dari 646 suka bar garuruwansu da ke kudancin Lebanon, sakamakon yadda ake kaiwa juna hari tsakanin mayakan kungiyar Hezbollah da sojojin Isra’ila.

Ita dai kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, ta kara tsaurara kai hare-harenta cikin Isra’ila, a wani yunkuri na taimakawa mayakan Hamas.

Lokacin wani hari da sojojin Isra'ira suka kai kudancin Lebanon a ranar 15 ga watan Oktoban 2023.
Lokacin wani hari da sojojin Isra'ira suka kai kudancin Lebanon a ranar 15 ga watan Oktoban 2023. AP - Hussein Malla

Tuni dai gwamnatin Isra’ila ta bada umarnin kwashe jama’arta da ke Arewacin kasar, duk da dai ba ta sanar da adadinsu ba.

Wasu alkaluma da Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP ya tattara, sun nuna cewar kimanin mutane 40 yawancinsu mayaka ne suka rasa rayukansu a yankin, amma dai akwai fararen hula 4 ciki harda dan jaridar Kamfanin Dillancin Labaran Reuters.

A bangaren Isra’ila akwai mutane hudu da suka mutu, ciki harda sojoji 3 da farar hula 1.

Matsayar kungiyar Tarayyar Turai EU kan batun kai kayan agaji 

Shugaban kare manufofin kungiyar Tarayyar Turai Josef Borrell, ya ce kungiyar na bukatar a gaggauta shigar da kayan agaji yankin Gaza, inda ya ce ministocin kasashen wajenta 27 za su tattauna batun tsagaita wuta don kai kayan agaji.

Jagoran diflomasiyyar Kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell
Jagoran diflomasiyyar Kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell AP

Matakan difulomasiya da ake dauka kan wannan rikici

A Talatar nan ce dai shugaban Faransa Emmanuel Macron zai ziyaraci fara ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, a wata makamanciyar ziyara da takwarorinsa na Amurka Joe Biden da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da kuma fara ministan Burtaniya Rishi Sunak suka kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.