Taron G77 ya bukaci soke basukan kasashe matalauta
Gwamnatocin duniya sun shiga rudu. Majalisar Dinkin Duniya, hukumomin Bretton Woods da kuma ta kasuwanci l'OMC sun rasa kimar da suke da ita a duniya, don haka bai kamata ba mu ci gaba da kasancewa a rarrabe », in ji shugaban kasar Beazil Lui Inaacio Lula Dasilva a lokacin da ya ke jawabi ga taron tattalin arziki na gungun G77 tare da China.
Wallafawa ranar:
Ya kamata kasashen duniya su kara hada karfi da karfe waje guda, domin samar da haske a kokarin da ake na samar da juyin juya hali ga sha’anin masana’antu a duniya, a cewar shugaban kasar mafi karfin tattalin ariziki a latin Amruka.
A jiya Assabar ne aka kawo karshen zaman taron gungun G77 da China a La Havane da ke kasar Cuba, inda da dama daga cikin wadanda suka yi jawabi a taron, suka bayyana rasahin samun dai daito a duniya, da matsalar annobar Covid19 ta kara fitarwa fili, da kuma bukatar ganin an ragewa kasashe matalauta basukan da ake binsu, domin samun damar amfani da kudin wajen yaki da dumamar yanayin a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu